Iran Ta Tsaida Wani Jirgin Ruwan Kasar Korea Ta Kudu Saboda Sabawa Dokokin Zirga-Zirga

2021-01-04 21:03:34
Iran Ta Tsaida Wani Jirgin Ruwan Kasar Korea Ta Kudu Saboda Sabawa Dokokin Zirga-Zirga

Sojojin ruwa na jumhuriyar musulunci ta Iran (JMI) sun tsaida wani jirgin ruwan daukar kaya mallakin gwamnatin Korea ta kudu a tekun farisa bayan da jirgin ya sabawa dokokin tsabtar tekuna. Majiyar muryar JMI ta nakalto sashen watsa labarai na rundunar sojojin ruwa ta kasar Iran mai suna Zulfikar tana fadar haka a yau Litinin.

Majiyar ta kara da cewa jirgin ruwan masi suna HANKUK CHEMI ya fito ne daga tashar jiragen ruwa ta Jubail ta kasar Saudia, dauke da sinadaran man fetur mai nauyin ton 7,200 kuma dauke da tutar kasar Korea ta kudu.
Labarin ya kara da cewa sau da dama jirgen ruwan ta karya dokokin kiyaye tsabtar taken na farisa, wanda ya tilastawa dakarun na kasar Iran kama shi.
Daga karshen labarin ya kara da cewa ma’aikatan jirgin sun hada da ‘yan kasashen Korea ta kudu, Myanmar da kuma Vetnam. A halin yanzu ana shirin gabatar da su a gaban kotu a nan kasar Iran.

019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!