Najeriya:Nasarawa United Ta Lallasa Headland 2-1 A Gasar NPFL

2021-01-04 20:48:52
Najeriya:Nasarawa United Ta Lallasa Headland 2-1 A Gasar NPFL

Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta lallasa kungiyar Headland ta babban birnin tarayyar 2-1 a gasar kwararrun ‘yan kwallon kafa na Najeriya NPFL a birnin Owerri a jiya Lahadi.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa Ohanachom da Hassan ne suka ciwa Nasarawa United kwallo guda-guda a rabin farko da na biyu. Har’ila yau kungiyar kwallon kafa ta Headland ta rama kwallo guda a minti na 63 a lokacinda Shedrack Oghali ya saka kwallo a ragan Nasarawa United a rabi na biyu, daga nan sun kasa ramawa har lokacin yayi masu halinsa.

019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!