An Gudanar Da Taron Tunawa Da Shekara Guda Da Shahadar Shahid Sulaimani A Nijeriya

2021-01-04 16:28:36
An Gudanar Da Taron Tunawa Da Shekara Guda Da Shahadar Shahid Sulaimani A Nijeriya

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar an gudanar da taron tunawa da shekara guda da shahadar tsohon kwamandan rundunar Qudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran, Janar Qasim Sulaimani da mataimakin kwamandan dakarun Hashd al-Sha’abi na kasar Iraki, Abu Mahdi al-Muhandis, a birnin Kano na kasar inda ya sami halartar bangarori daban-daban na al’ummar musulmi.

Rahotannin sun ce taron dai wanda mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky, jagoran harkar Musulunci a Nijeriyan ne suka shirya shi an gudanar da shi ne a daya daga cikin masallatan birnin na Kano da ke arewacin Nijeriya inda aka gabatar da lakcoci da jawabai.

A jawabin da ya gabatar a wajen taron, Dakta Sunusi Abdulkadir, wakilin ‘yan’uwa mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a garin na Kano, yayi karin haske dangane da irin sadaukarwar da wadannan shahidai guda biyu wato Shahid Qasim Sulaimani da Shahid Abu Mahdi Al-Muhandis suka yi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan al’ummomin yankin Gabas ta tsakiya da kuma fada da kungiyoyin ta’addanci irin su Daesh (ISIS) da sauransu. Kamar yadda kuma yayi karin bayani dangane da irin dabi’u da kuma halayensu.

Har ila yau kuma Dakta Sunusi Abdulkadir, yayi karin bayani dangane da irin makircin da ‘yan mulkin mallaka suka kulla wajen kafa kungiyoyin ta’addanci da yankini Gabas ta tsakiyan, da kuma irin rawar da wadannan shahidai biyu suka taka wajen kawo karshen wannan makircin, wanda ya ce hakan na daga cikin dalilan da suka sanya Amurka da kawayenta fusata da kuma aiwatar da wannan danyen aiki na kisan gillan da suka yi wa shahidan biyu da wadanda suke tare da su.

Taron dai wanda baya ga magoya bayan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da suka halarta, har ila yau kuma ya samu halartar wasu mabiya tafarkin Ahlussunna na garin na Kano, lamarin da ke nuni da irin matsayi da girman da wadannan shahidai biyu suke da shi a zukatan al’ummar musulmi na duniya.

A ranar 3 ga watan Janairun shekara ta 2020 ne dai sojojin Amurka suka kai hari ga motocin da suke dauke da Shahid Qasim Sulaimani da Shahid Abu Mahdi Al-Muhandis da wasu daga cikin masu kula da lafiyarsu a kusa da filin jirgin saman Bagadaza na kasar Iraki lamarin da yayi sanadiyyar shahadarsu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!