Kasashen Masar, Sudan Da Habasha Sun Amince Kara Tattaunawa Kan Madatsar Ruwan Nilu

2021-01-04 14:36:59
Kasashen Masar, Sudan Da Habasha Sun Amince Kara Tattaunawa Kan Madatsar Ruwan Nilu

Ministocin harkokin waje da noman rani na kasashen Masar da Sudan da Habasha, suka amince su gudanar da zagayen tattaunawa na tsawon mako guda, don duba wasu muhimman sassa da ma batutuwa da ake takaddama kan su, game da babbar madatsar ruwan nan ta kasar Habasha(GERD) da ake rikici a kanta.

Amincewa a gudanar da sabon zagayen tattaunawar, na zuwa ne bayan wata ganawa ta kafar bidiyo da ministoci daga kasashen uku suka yi, game da cikewa da kuma fara aiki da madatsar ruwan, karkashin kulawar kungiyar tarayyar Afirka(AU).

Yayin ganawar, kasar Masar ta jaddada bukatar cimma yarjejeniya, kafin a fara zagaye na biyu na aikin cike wurin adana ruwa na madatsar ruwan, abin da ke nuna cewa, bakin kasashen uku ya zo daya kan wannan batu.

A shekara 2011 ne dai, kasar Habasha ta fara aikin gina madatsar ruwan, yayin da Masar ta nuna damuwa cewa, aikin madatsar ruwan yana iya shafar cubik mita biliyan 55.5 na kason ruwan da take samu daga kogin Nilu a duk shekara. Ita ma kasar Sudan a baya-bayan nan ta nuna irin wannan damuwa game da illar da madatsar ruwan ka iya haifar mata.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!