Afrika Ta Kudu Za Ta Yi Wa Al’ummarta Kashi 67% Riga Kafin Korona Cikin 2021

2021-01-04 14:31:16
Afrika Ta Kudu Za Ta Yi Wa Al’ummarta Kashi 67% Riga Kafin Korona Cikin 2021

Gwamnatin Afrika ta Kudu, ta kudiri anniyar yi wa al’ummarta kashi 67 cikin dari riga kafin cutar korona.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da yawan masu kamuwa da cutar ke dada karuwa saboda bullar sabon nau’in cutar ta korona.

A don hake ne a cewar gwamnatin Afrika ta Kudun zatayi wa al’ummar kasar miliyan arba’in riga kafin cutar.

Yanzu haka dai gwamnatin kasar na tattaunawa da game da kamfanonin harhada magunguna na Pfizer, AstraZeneca, da kuma gwamnatocin Rasha da China domin sayen riga kafi.

Afrika ta kudu, dai ita ce wata kasa ta nahiyar Afrika da annobar korona ta fi wa illa inda take da mutane sama da miliyan guda sai kuma dubu talatin da cutar ta yi ajalinsu.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!