Nijar : Shugaba Isufu, Ya Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Fararen Hula
2021-01-04 14:28:32

Shugaba Isoufou Mahammadu na jamhuriyar Nijar, ya yi tir da allawadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a wasu kauyuka biyu dake jihar Tillaberi a iyaka da kasar Mali.
A wani sako da ya aike a shafinsa na twitter, shugaba Isufu, ya kuma isar da sakon ta’aziyya ga iyallen wadanda lamarin ya rusa dasu.
Rahotanni daga kasar dai sun ce gomman fararen hula ne dai suka rasa rayukansu a harin na ranar Asabar.
A jawabinsa da ya gabatar a jajabirin shiga
sabuwar shekara, shugaba Isufu, ya sha alwashin ganin bayan ayyukan ta’addanci
da kasar ke fama dasu.
024
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!