​An Bankado Wani Sauti Da Aka Nada Trump Na Neman Aringizon Kuri’u A Jihar Georgia

2021-01-04 10:32:59
​An Bankado Wani Sauti Da Aka Nada Trump Na Neman Aringizon Kuri’u A Jihar Georgia

An bankado wani bayani wanda aka nadi sautinsa, wanda a ciki Donald Trump yake umartar sakataren gwamnatin Jihar Georgia, da ya samu karin kuri’u da za su ba shi damar sauya akalar sakamakon zaben shugaban kasar.

Jaridar Washington Post ta bayar da rahoton cewa, ta samu sautin na Donald Trump a lokacin da yake neman sakataren jihar Georgia Brad Raffensperger, da ya samo masa karin kuri’u 11,799, domin canja sakamakon zaben shugaban kasa.

Trump ya ce da Brad Raffensperger wanda jam’iyyarsu daya da Trump wato Republican, abin da nake bukata yanzu kawai shi ne kuri’u 11,799, idan na same su to komai zai canja.

To sai a nasa bangaren Brad Raffensperger yaki baiwa Trump hadin kai domin aikata wannan badakala, inda ya sheda wa Trump cewa, ranka ya dade babu wani kure a cikin sakamakon zaben da aka bayar a Georgia, wanda ya tabbatar da cewa Joe Biden ne ya yi nasara a jihar.

Daga karshe Trump ya yi masa barazana matukar dai bai aiwatar da abin da yake bukata ba, yayin da shi kuma ya dage a kan bakansa na kin aiwatar da umarnin na Trump.

Fadar shugaban kasar Amurka taki ta ce uffan kan wannan tabargaza da aka bankado wadda Trump ya tafka, yayin da su ma hukumomi a jihar ta Georgia ba su komai kan lamarin ba.

A ranar 20 ga wannan wata na Janairu ne za a rantsar da zababben shugaban kasar ta Amurka Joe Biden a matsayin sabon shugaban kasar Amurka.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!