​Zarif : ‘Yan Ta’addan Daesh Da Iyayen Gidansu Ne Kawai Suka Amfana Da Kisan Qassem Sulaimani

2021-01-04 10:05:09
​Zarif : ‘Yan Ta’addan Daesh Da Iyayen Gidansu Ne Kawai Suka Amfana Da Kisan Qassem Sulaimani

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan Daesh da iyayen gidansu ne kawai suka amfana da kisan Qassem Sulaimni.

A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na twitter, Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, a yankin gabas ta tsakiya babu wanda ya amfana da kisan Qassem Sulaimani sai ‘yan ta’addan Daesh da iyayen gidansu.

Ya ce Sulaimani ne ya zama babban karfen kafa tare da hana ‘yan ta’adda sakat a yankin gabas ta tsakiya, musamamn ‘yan ta’addan daesh wadanda suke a matsayin babbar barazana ga al’ummomin yankin, inda sadaukarwar da ya yi ce ta karya lagon ‘yan ta’addan a cikin Syria da Iraki.

Zarif ya yi ishara da cewa, kisan gillar da Amurka ta yi wa Qassem Sulaimania daidai lokacin day a murkushe Daesh ya karya lagonta ayankin gabas ta tsakiya, hakan ya kara saka alamar tambaya kan alakar da ke tsakanin ‘yan ta’addan na daesh da Amurka.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!