Sayyid Nasrullah: Qassem Sulaimani Ya Shiga Cikin Gwaraza Na Tarihi Har Abada

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana Qassem Sulaimani a matsayin gwarzon da tarihi ba zai manta da shi ba.
A cikin wani jawabi wanda ya gabatar
a daren yau Lahadi, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon,
dangane da cikar shekara daya da kisan Qassem Sulaimani da Abu Mahdi
Almuhandis, Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, wadannan gwaraza ne na
tarihi.
Ya ce Qassem Sulaimani ya bayar da
gagarumar gudunmawa a bangarori daban-daban wajen taimaka al’ummomi da
suke karkashin zalunci a kasashe daban-daban, wanda hakan ba a bu ne da yake
boye ga kowa ba a duniya.
Ya e saboda irin wannan jarunta tasa
ne da kuma gwagwarmaya da zalunci da taimakon raunana, masu zalunci da suke
zaluntar raunana suka dauki matakin ganin bayansa ta hanyar kashe shi.
Dangane da Abu Mahdi Muhandis kuwa,
Sayyid Nasrullah ya bayyana shi a matsayin abokin tafiyar Qassem Sulaimani a
cikin gwagwarmayarsa, wanda kuma irin gudunmawar da Muhandis ya bayar wajen
fatattakar ‘yan ta’adda a cikin Iraki da Syria, da kuma dawo wa wadannan
kasashe da tsaronsu, babban lamari ne a cikin tarihin rayuwarsa.
Dangane da halin rashin tabbas da
ake ciki a yankin gabas ta tsakiya a ranakun karshe na mulkin Trump kuwa,
Nasrullah ya bayyana cewa, dole ne a kara zama cikin shirin fuskantar kowane
irin aikin wawanci da Trump ka iya aikatawa a gabas ta tsakiya kafin ya bar
mulkin Amurka.
015