Dubban Mutane Sun Yi Cincirindo A Tsakiyar Birnin Bagadaza Na Iraki Suna Yin Kira Ga Amurka Da Ta Fice Daga Kasarsu

2021-01-03 19:30:18
    Dubban Mutane Sun  Yi Cincirindo A Tsakiyar Birnin Bagadaza  Na Iraki Suna Yin Kira Ga Amurka Da Ta Fice Daga Kasarsu

Irakawan sun yi cincirindo ne a dandalin shahidai dake cikin birnin Bagadaza domin tunawa da zagayowar shekara daya da shahadar Laftanar Janar Kassim Sulaimani da kuma Abu Mahdi al-Muhandis da Amurka ta yi wa kisan gilla.

A cikin wasu biranen Iraqi da dama an yi irin wannan gangamin na kira ga Amurka da ta tattara yanata, yanata ta fice daga cikin kasar baki daya.

Har ila yau, mutanen sun rika yin jinjina ga shahidan da suka kwanta a fagen dagar fada da ‘yan ta’adda, da kuma manyan kwamandojin da Amurka ta yi wa kisan gilla a shekarar da ta gabata.

A ranar 3 ga watan Janairu na shekarar da ta gabata ne dai Amurka ta yi wa janar kassim Sulaimani da kuma Abu Mahadi al-muhandis a kusa da filin saukar jiragen sama na birnin Bagadaza.


013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!