Sojojin Kasar Faransa 2 Sun Halaka A Kasar Mali

2021-01-03 19:27:09
  Sojojin Kasar Faransa 2 Sun Halaka A Kasar Mali

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Mali sun bayyana cewa sojojin kasar Faransa 2 sun halaka ne a yayin da motarsu ta taka wani abu mai fashewa da aka ajiye akan hanyar da take wucewa.

Daga cikin sjojin da su ka halaka da akwai mace, kamar yadda rahoton ya nuna.

Ma’aikatar sojan kasar Faransa da ta fitar da sanarwa akan abinda ya faru ta kara da cewa; A yankin Menaka ne motar sojan ta taka nakiyar da ta tashi da ita, kuma matar soja mai suna Huynh ita ce mace ta farko da aka kashe tun da Faransa ta fara jagorantan yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

A cikin wannan makon kadai sojojin faransa 5 ne aka kashe, bayan da wasu uku su ka halaka sanadiyyar tashin nakiliyar da aka dasa a gefen hanya.

Wata majiyar sojan Mali ta ambaci cewa a ranar Asabar da ta gabata, wasu mutane da ba a kai ga tantance su ba, sun kashe fararen 58 a cikin kasar Nijar.

Majiyar ta shaida wa kafar watsa labarun kasar Rasha ta “Sputnik” cewa maharan sun kashe mutane 58 a garin Tusho Mbang da ke kan iyakar Nijar da Mali.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!