Kungiyar Boko Haram Ta Yi Awon Gaba Da Matafiya 50 Akan Hanyar Damaturu Zuwa Maiduguri

2021-01-03 19:24:23
Kungiyar Boko Haram Ta Yi Awon Gaba Da Matafiya 50 Akan Hanyar  Damaturu Zuwa Maiduguri

Rahotanni daga kasar ta Nigeria sun ce, baya ga mutane 50 din da kungiyar mai dauke da makamai ta yi awon gaba da su, ta kuma hada da wani ma’aikacin agaji na MDD Abubakar Garba Idris.

Kama mutanen da aka yi a wannan lokacin ya biyo bayan kwatankwacinsa da ya faru makwanni biyu da su ka gabata inda aka yi awon gaba da matafiya 35 mafi yawancinsu mata da kananan yara a tsakanin Jakana da Beni Sheikh.

Shedun ganin ido sun ce maharani sun datse hanyar ne da misalin karfe; 8;25 na safe a kusa da garin Matari daura da garin Jakana a jiya Asabar.

Gwamnan Jihar Borni Babagana Zulum ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ina day a dorawa jami’an tsaro laifin kin yin abinda ya kamata domin bayar da kariya ga rayukan mutane da dukiyoyinsu.


013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!