Janar Kasim Sulaimani Ya Taka Gagarumar Rawa Wajen Tabbatar Da Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Wakilin Jihadul Islami a Tehran ya
bayyana janar Kasim Sulamini da cewa shi ne ya taka wa kasashen yamma da
yahudawa gami da ‘yan korensu burki a gabas ta tsakiya.
A cikin bayaninsa a jiya wakilin
Jihadul Islami ta Falastinu a Tehran ya bayyana cewa, ko shakka babu Kasim
Sulamini ya bayar da gudunmawa a bangarori daban-daban ga al’ummomin yankin
gabas ta tsakiya.
Ya ce babbar gudunmawa da ya bayar
ga al’ummar wannan yanki ko sun sani ko ba su sani ba, ita ce ya hana wa
kasashen yammacin turai da yahudawan sahyuniya gami da ‘yan korensu na yankin
gabas ta tsakiya burki a gabas ta tsakiya, kafa abin da suke kira sabuwar gabas
ta tsakiya.
Ya ce baya ga haka kuma, al’ummar Falastinu
sun san irin gudunmawar da ya bayar wajen hana yahudawan sahyuniya cimma
burinsu na mamaye yankin zirin Gaza, inda bai taba gajiyawa ba wajen taimaka ma
falastinawa ‘yan gwagwarmaya da makamai domin su kare kansu da kasarsu.
Haka kuma yakin Lebanon na shekara
ta 2006, shi ne gishikin nasarar da aka samu kan yahudawa wajen murkushe
kaidinsu a kan al’ummar Lebanon, kamar yadda ya bayar da gudunmawa wajen korar
yahudawan Isra’ila a cikin shekara ta 2000 da suka mamaye kudancin Lebanon,
inda suka fita babu shiri.
Baya ga haka kuma shi ne ya taka
gagarumar rawa wajen karya lagon 'yan ta'addan takfir a Syria da Iraki da kuma
Lebanon.
015