Najeriya: Mutane 576 Ne Suka Kamu Da Cutar Korona A Jiya Asabar
2021-01-03 14:39:03

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 576 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar
ranar Asabar sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –277, FCT-90, Oyo-51,
Nasarawa-49, Sokoto-23, Anambra-14, Bauchi-11, Imo-11, Kano-11, Edo-10,
Plateau-10, Ogun-9, Osun-5, Jigawa-3, Rivers-2.
Yanzu mutum 89,163 suka kamu da
cutar a Najeriya, mutum 74,789 sun warke, 1,302 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu
mutum 13,072 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Juma’a, mutum 1,074 suka kamu a Najeriya, , jihohin Legas Kaduna, Rivers, Gombe, Kano da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Jami’an kula da lafiya, sun bayyana
cewa a matsayin su na wadanda ke sahun farkon saida rai domin su ceto rayukan
wasu, su na bukatar karin kudaden alawus.
015
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!