Iran : Ana Juyayin Shekara Guda Da Shahadar Janar Qassem Suleimani

2021-01-03 10:10:21
Iran : Ana Juyayin Shekara Guda Da Shahadar Janar Qassem Suleimani

A Iran, ana juyayin cika shekara guda da kisan Janar Qassem Sulaimani, wanda ya yi shahada a wani hari da Amurka ta kai wa tawagar motocinsa a Iraki a ranar 3 ga watan Janairun 2020.

Kisan da akayi wa Janar Sulaimani, ya bakantawa al’ummar Iran rai matuka, duba da matsayin da kimar da Sulaimanin ya ke da shi a idon Iraniyawa dama wasu kasashen yankin.

Laftana janar Qassem Sulaimani, ya yi shahada ne a wani harin jirgi marar dreba da shugaba Trump na Amurka ya bada umarnin kaiwa tawagar motocinsa a kusa da filin jirgin saman Bagadaza na kasar Iraki a rana irin ta yau a 2020.

Daga cikin wadanda sukayi shahada a harin, har da Abu Mahdi Al’Mouhandis, kwamandan rundinar Hashdu Sha’abi ta kasar Iraki da wasu dake tare dasu.

Iran dai na mai ci gaba da shan alwashin daukar fansa akan kisan da Amurka ta yi wa janar din nata, bayan martanin data mayar ta hanyar kai hare haren makamai masu linzami a sansanin sojin Amurka dake Iraki.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!