Nijar : Jam’iyya Mai Mulki Ce Ke Da Rinjaye A Majalisar Dokoki

2021-01-03 10:05:51
Nijar : Jam’iyya Mai Mulki Ce Ke Da Rinjaye A Majalisar Dokoki

Jam’iyyar PNDS tarraya mai mulki a Jamhuriyar NIjar, ta samu gagarimin rinjaye a majalisar dokokin kasar, bayan lashe zaben shugaban kasar da za’a je zagayensa na biyu da tazara mai yawa.

PNDS, ta samu kujera 80 daga cikin 166, yayin da jam’iyyar Moden Lumana ta samu 19, sai kuma MNSD-nassara da MPR Jamhuriya suka samu guda 13 ko wannensu.

Saidai wasu jam’iyyun sun ce zasu shigar da korafi saboda zargin magudi da aikata ba daidai ba a zaben da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata.

A jiya ne Hukumar zabe ta kasa a jamhuriyar Nijar, ta sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar da aka kada kuri’arsa a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata.

Sakamakon da hukumar ta fitar a safiyar wannan Asabar ya nuna cewa dan takarar jam’iyyar PNDS-Tarrayya mai mulki ne cewa da Malam Bazoum Mohamed, ne kan gaba, da kashi 39,33 cikin dari, kwatankwacin kuri’in kimanin miliyan 1,9 yayin da tsohon shugaba Alhaji Mahamane Usman , na jam’iyyar RDR Canji ne ke biye masa da kashi 16,99 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada.

Hakan dai yana nufin za’a je zagaye na biyu a zaben shugabancin kasar a karshen watan Fabrairu mai zuwa, tsakanin Bazoum Mohamed da Mahamane Usman.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!