Akwai Kyakyawan Fata Game Da Yarjejeniyar Cinikayya Ta Afrika

2021-01-03 09:59:06
Akwai Kyakyawan Fata Game Da Yarjejeniyar Cinikayya Ta Afrika

Ana kara sa ran dunkulewar nahiyar Afrika yayin aka fara cinikayya karkashin yarjejeniyar nan ta ciniki marar shinge.

An fara cinikayya karkashin yarjejeniyar ce a ranar 1 ga watan Janairun shekarar nan da muka shiga, yayin da ake kara sa ran ganin dunkulewar nahiyar.

Zuwa yanzu, yarjejeniyar wadda aka kaddamar a watan Maris na 2018 a birnin Kigalin Rwanda, ta samu kasashen nahiyar 54 da suka rattaba hannu a kai, lamarin da ya samar da sabuwar fata da murna ta fuskar inganta cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar da kuma saukaka rayuwa da bunkasa ayyukan masana’atu.

Eritrea ce kasa daya tilo da bata sa hannu kan yarjejeniyar ba.

Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ke shugabantar Tarayyar Afrika a wannan karo, ya jaddada cewa, yarjejeniyar yankin cinikayyar cikin ‘yanci, za ta samar da gagarumin sauyi ga tattalin arzikin nahiyar.

A cewar hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD (UNECA), yarjejeniyar na da karfin bunkasa matsayin cinikayya tsakanin kasashen nahiyar da sama da kaso 52, ya zuwa shekarar 2022.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!