Rouhani:Korona Jarrabawace Ga Mutanen Duniya Da Shuwagabanninsu

2021-01-02 20:29:03
Rouhani:Korona Jarrabawace Ga Mutanen Duniya Da Shuwagabanninsu

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani, ya bayyana cewa cutar korona wata jarrabawa ce ga mutanen duniya musamman ga shuwagabannin wadannan kasashe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a safiyar yau Asabar, a taron kwamitin yaki da cutar ta korona na kasa a nan Tehran.

Rouhani ya kara da cewa mutanen kasar Iran sun bada hadin kai sosai, ga shirye-shiryen kwamitin yaki da cutar ta korona, don dakile yaduwar cutar, musamman a lokacin da cutar ta sake dagawa a koro na uku a duk fadin kasar.

Shugaban ya yabawa ma’aiktan jinya, wadanda suka hada da likitoci, jami’an jinya da kuma jami’an gwamnatin kasar, kan gudumawar da suka bayar don ganin an dakile cutar.

Har’ila yau shugaban ya yabawa jagoran juyin juya halin musulunci wanda ya bada shawarori da dama ga gwamnati, da kuma kwamitin yaki da cutar tun bayar bullarta a farkon shekarar da ta gabata.

Daga karshe shugaban ya yi kira ga mutanen kasar Iran da su ci gaba da bada hadin kai don ganin cutar bata sake dawowa ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!