Hamas:Ana Kokarin Don Farfado Da Tattaunawa Tsakanin Kungiyoyin Falasdinawa

2021-01-02 20:09:54
Hamas:Ana Kokarin Don Farfado Da Tattaunawa Tsakanin Kungiyoyin Falasdinawa

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas ta Falasdinu, Isma’il Haniyah ya bayyana cewa akwai kokarin da ake yi na sake farfado da tattaunawa tsakanin kungiyoyin Falasdinawa na ciki da wajen kasar, don fuskatantar Amurka, Isara’ila da kuma kawayensu na kasashen larabawa.

Haniyeh ya kara da cewa yin haka zai hana wadannan kasashe cimma mummunar manufofinsu na hana falasdinawa mallakar kasarsu, ko dawowa cikin kasarsu da kuma mallakar wurare masu tsarkin da suke cikin kasar.

Cibiyar yada labarai ta Falasdinawa ta nakalto Haniyeh yana cewa a halin yanzu an fara tuntumar kungiyoyin Falasdinawa na ciki da wajen kasar wadanda suka hada da PLO don ganin an farfado da tattaunawar nan ba da dadewa ba.

A cikin watan satumban shekarar da ta gabata ce Isma’ila Haniyah ya yi kira ga Falasdinawa su dinke barakar da ke tsakaninsu don cimma manufa ta hadin kan kasar da kuma fuskantar makiyansu na gaskiya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!