Falasdinu:An Fidda Rahoton Yawan Barnan Da Isra’ila Ta Yi A Shekara Ta 2020 A Birnin Kudus

2021-01-02 20:02:06
Falasdinu:An Fidda Rahoton Yawan Barnan Da Isra’ila Ta Yi A Shekara Ta 2020 A Birnin Kudus

Cibiyar yada labarai ta Ainul Helwa ta bada bayanai dangane da barnan da haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ta yi a birnin Qudus a shekarar da ta gabata.

Cibiyar yada labaran ta bada wannan sanarwan ce, a yau Asabar ta kuma kara da cewa yahudawan sun kai Falasdinawa 6 ga shahada ta harbi da bindiga a cikin birnin a shekara ta 2020.

Banda haka labarin ya kara da cewa yahudawan sun kori falasdinawa da dama daga birnin na wani lokaci, kama daga kwana biyu zuwa watannin 6. Har’ila yau yahudawan Sahyoniyya sun kona masallacin “Badraini” a cikin birnin, sannan sun yi rubutun batanci da nuna wariya a kan katangun masallacin.

Rahoton ya kara da cewa gwamnatin yahudawan sahyoniyya sun kama mutane 1,979 a cikin shekarar da ta gabata a birnin, sannan 8 daga cikinsu yara ne ‘yan kasa da shekara 12 a duniya, sai kuma matasa 344 sannan maza 100.

Daga cikin wadanda suka kama akwai Sheikh Ikramah Sabri shugaban majalisar musulunci ta birnin Qudus. Daga karshe rahoton ya ce yahudawan sun rusa gidajen Falasdinawa 193 a shekarar da ta gabata a birnin Kudus.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!