Iran:Nazemi Ta Ce Wasan Barcelona Ce Ta Fi Bata Wahala A Aikin Alkalincin Wasanni
2021-01-02 19:53:33

Wata
alkaliyar wasan Futsal, (ko referee) mai suna Gelareh Nazemi ‘yar kasar Iran ta
bayyana cewa gasar wasan kwallon kafa tsakacin Barcelona da Shenzhen na kasar
Sin ya fi bata wahala a tarihin rayuwarta na alkalancin wasannin kwallon kafa.
Kamfanin
dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa kungiyar wasannin Fursal
ta “Futsal Planet” ta sanya sunan Nazemi cikin zababun alkalan wasannin kwallon
kafar ta futsal 10, na kungiyar , kuma na shekara ta 2020 da ta gabata.
Nazemi ta
kara da cewa da alamun kungiyar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fara amincewa
da alkalan wasannin kasar Iran mata, musamman ganin yadda ta sanya sanayen wasu
alkalan wasan kwallon kafa na mata don alkalanci a gasar FIFA ta shekara 2023.
Nazemi diyar shekara 39 a duniya ta kara da cewa ta yi alkalancin wasannin na tsawon shekaru 19, amma ba wacce ta bata wahala kamar wasan kwallon kafa ta maza, tsakanin kungiyar Barcelo da Shenzhen ta Hong Kong, kuma ita ce wasar da tafi burge ta.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!