Iran Na Shirin Fara Sarrafa Sinadarin Uranium Zuwa Kaso 20 Cikin 100

2021-01-02 15:03:05
Iran Na Shirin Fara Sarrafa Sinadarin Uranium Zuwa Kaso 20 Cikin 100

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta aike wa da hukumar hana yaduwar makamman nukiliya ta duniya cewa da IAEA wasika wacce a ciki ta bayyana anniyarta na fara sarrafa sinadarin uranium zuwa kaso ashirin cikin dari.

Da yake bayyana hakan a shiri da aka gabatar a gidan talabijin din kasar, shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran, Ali Akbar Salehi, ya ce komi ya kammala game da wannan niyyar, kawasi umarnin shugaban kasar Hassan Rohani suke jira.

Game da fara shirin na sarrafa sinadarin na uranium zuwa kashi 20 cikin 100 a ma’aunin inganci M. Salehi, ya ce, sun riga sun mika wasika ga wakilin Iran a Vienna domin ya mika ta ga hukumar IAEA.

Kuma game da hakan wakilan hukumar zasu zo Iran domin sanya ido a sabbin na’urorin da za’a dora.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!