Za’a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasar Nijar

2021-01-02 14:59:46
Za’a Je Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasar Nijar

Hukumar zabe ta kasa a jamhuriyar Nijar, ta sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar da aka kada kuri’arsa a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata.

Sakamakon da hukumar ta fitar a safiyar wannan Asabar ya nuna cewa dan takarar jam’iyyar PNDS-Tarrayya mai mulki ne cewa da Malam Bazoum Mohamed, ne kan gaba, da kashi 39,33 cikin dari, kwatankwacin kuri’in kimanin miliyan 1,9 yayin da tsohon shugaba Alhaji Mahamane Usman , na jam’iyyar RDR Canji ne ke biye masa da kashi 16,99 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada.

Hakan dai yana nufin za’a je zagaye na biyu a zaben shugabancin kasar a karshen watan Fabrairu mai zuwa, tsakanin Bazoum Mohamed da Mahamane Usman.

‘Yan takaran dake biye masu sun hada da Seyni Omar, na jam’iyyar MNDS Nassara, sai kuma Albade Abuba na MPR-Jamhuriya, sai kuma Ibrahim Yakuba na MPN-kishin kasa.

‘Yan takara 30 ne dai suka fafata a zaben.

Yanzu dai hukumar zaben kasar za ta mika sakamakon ga kotun tsarin mulki domin neman amincewarta kafin a je zagaye na biyu.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!