Najeriya : Buhari Zai Ba Da Muhimmanci Ga Harkokin Tsaro, Da Tattalin Arziki A 2021

2021-01-02 14:57:00
Najeriya : Buhari Zai Ba Da Muhimmanci Ga Harkokin Tsaro, Da Tattalin Arziki A 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali kan muhimman fannoni a karkashin ajandarsa ta tabbatar da tsaro, raya tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa, domin karfafa fatan ‘yan Najeriya “a matsayin kasa dunkulalliya’

A jawabinsa albarkacin murnar shiga sabuwar shekara, Buhari ya bayyana cewa, shekarar 2020 ta kasance mai matukar wahala ga Najeriya, yayin da talauci, da tashe-tashen hankula da sauran kalubale suka dabaibaye kokarin gwamnati, na aiwatar da manufofin inganta jin dadin jama’a, da wadanda suka shafi zuba jari da ka iya sauya al’amura a harkokin jin dadin ‘yan Najeriya.

Shugaban ya kuma yi alkawarin kara zage damtse da sake fasalta hukumomin tsaro da jami’ an soji da na ‘yan sanda, da nufin kara karfinsu na tunkarar barazanar kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da masu aikata manyan laifuffuka a wasu sassan kasar.

A bangaren tattalin arziki, Buhari ya ce, zai mayar da hankali wajen farfado da tattalin arziki ta hanyar ajandar kasar ta fadada hanyoyin tattalin arziki, dake goyon bayan manufar samar da isasshen abinci a cikin kasa.

A fannin yaki da cin hanci da rashawa kuwa, shugaban ya ce, gwamnatinsa ta himmatu wajen ci gaba da kawar da matsalar ta cin hanci, ta hanyar yin hadin gwiwa da dukkan sassa na gwamnati.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!