An Kaddamar Da Yankin Cinikayya Maras Shinge Na Nahiyar Afirka

2021-01-02 14:54:12
An Kaddamar Da Yankin Cinikayya Maras Shinge Na Nahiyar Afirka

An kaddamar da ciniki marar shinge na nahiyar Afirka, al’amarin da ya alamta cewa kasashen Afirka sun samu babban ci gaba wajen kafa wata babbar kasuwar hadaka ta bai daya.

An kaddamar da shirin ne a jiya Juma’a kamar yadda aka tsara a ranar 1 ga watan Janauru na shekara 2021 din nan da muka shiga.

Kwararru na ganin cewa, kaddamar da cinikayyar, zai taimaka sosai wajen farfado da tattalin arzikin Afirka da sauya kalubale zuwa damammaki, duk da yadda annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa.

Shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka, kana shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya nuna cewa, idan aka yi nasarar aiwatar da yarjejeniyar, ya kamata a shawo kan kalubaloli daban-daban da kasashen Afirka suke fuskanta a fannonin da suka shafi siyasa da zaman rayuwa gami da tattalin arziki. A cewarsa, ya kamata a daidaita matsalolin da suke tattare da talauci da rashin daidaito da kuma rashin ci gaba.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!