​Isma’il Qa’ani: Mai Yiwuwa Martani Kan Amurka Ya Zama Daga Cikin Kasar Ne

2021-01-02 10:31:42
​Isma’il Qa’ani: Mai Yiwuwa Martani Kan Amurka Ya Zama Daga Cikin Kasar Ne

Babban kwamandan rundunar Quds a Iran Janar Isma’il Qa’ani ya bayyana cewa, mai yiwuwa daukar fansa ya zama a cikin kasar Amurka ne.

Janar Isma’il Qa’ani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron tunawa da kisan gillar da Amurka ta yi Qassem Sulaimani, tsohon babban kwamandan rundunar Quds reshen IRGC da ke gudanar da ayyukan soji a wajen kasar Iran, da kuma Abu Mahdi Almuhandis, mataimakin babban kwamandan Hashd Al-shaabi a Iraki.

Ya ce batun daukar fansa magana ce ta lokaci kawai, amma abu ne wanda babu makawa a kansa, kuma wannan daukar fansa za ta iya zama a hannun su kansu Amurkawan domin kuwa komai zai iya faruwa a kan mutumin da ya cutar da kowa domin maslaharsa.

Ma’aikatar tsaron kasar Amurka dai ta bayyana cewa, shugaban Amurka mai barin gado ne da kansa ya bayar da umarnin kisan Qassem Sulaimani, kuma an yi amfani da jiragen yaki marassa matuki ne mallakin ma’aikatar tsaron kasar Amurka wajen aiwatar da kisan a cikin kasar Iraki a ranar 1 ga watan Janairun 2020.

A jiya an gudanar da taruka a cikin kasashen Iran, Iraki, Lebanon, Syria Falastinu, domin tunawa da Qassem Sulaimani da kuma Abu Mahdi Almuhandis, tarukan da malamai da wakilan kungiyoyi da ma jami’an gwamnati suka halarta.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!