Najeriya: Mutane 1074 Suka Kamu Da Corona A Ranar 1 Ga Watan Janairun 2021

Hukumar yaki da cututtuka masu
yaduwa a Najeriya NCDC ta sanar da cewa, mutane 1074 da suka kamu da cutar
Korona a fadin kasar a ranar jiya Juma’a.
Jaridar Premium Times ta bayar da
rahoton cewa, alkaluman da hukumar NCDC ta fitar a ranar Juma’a sun nuna cewa
Legas ta samu karin mutane –642, Kaduna-92, Rivers-78, FCT-66, Gombe-66,
Kano-35, Ogun-31, Katsina-22, Filato-20, Abia-7
Niger-4, Oyo-4, Akwa Ibom-3, Delta-2 da Osun-2
Bisa rahoton hukumar ta NCDC yanzu
mutane 88,587 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 74,373 sun warke, 12,562 sun
rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,974 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Alhamis jajibirin shekara ta
2021, mutane 1,031 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Nasarawa, Bauchi, Kano
da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da
mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 30,830, FCT –11,771, Oyo – 3,943, Edo
–2,870, Delta –1,888, Rivers 3,553, Kano –2,297, Ogun–2,524, Kaduna –5,328,
Katsina -1,636, Ondo –1,811, Borno –796, Gombe –1,272, Bauchi –1,009, Ebonyi
–1,107, Filato – 4,859, Enugu –1,382, Abia – 1,000, Imo –755, Jigawa –403,
Kwara –1,414, Bayelsa –519, Nasarawa –799, Osun –1,014, Sokoto –357, Niger –
417, Akwa Ibom – 437, Benue – 532, Adamawa – 391, Anambra – 308, Kebbi – 173,
Zamfara –112, Yobe – 187, Ekiti –410, Taraba- 217, Kogi – 5, da Cross Rivers –
169.
A Najeriya dai ana samun hau-hawar alkaluman wadanda suke kamuwa da cutar ta corona a halin yanzu. Abin ya kai ga har an fara rufe makarantu da kuma saka dokoki domin kiyaye wa.
015