​Allah Ya Yi Wa Ayatollah Mohammad Mesbah Yazdi Rasuwa

2021-01-02 09:23:14
​Allah Ya Yi Wa Ayatollah Mohammad Mesbah Yazdi Rasuwa

A jiya ne Allah ya yi wa daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Iran Ayatollah Mohammad Mesbah Yazdi rasuwa a jiya.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a jiya ne 1 ga watan juanairun 2021 Allah ya yi wa babban malamin addini na kasar Iran Ayatollah Mohammad Mesbah Taqi Yazdi rasuwa bayan fama da rashin lafiya yana shekaru 86 a duniya.

An haifi Ayatollah Mohammad Mesbah Taqi Yazdi a garin Yazd na kasar Iran a shekara ta 1935, ya yi karatun addini mai zurfi, daga cikin malamansa akwai Ayatollah Burujardi, Ayatollah Bahjat da kuma Imam Khomaini.

Ya yi rubuce-rubucen littafai na addini masu tarin yawa a bangarori daban-daban na ilmomin addini, da hakan ya hada da tafsirin kur’ani mai tsarki.

Baya ga haka kuma Ayatollah Mesbah Yazdi ya shahara a bangaren ilimin falsafa da irfani, inda ya yi rubuce-rubuce masu yawa a wannan fage.

Haka nan kuma ya kasance daga cikin malaman da suka kalubalanci mulkin kama karya na sarakunan Pahlawiya a Iran, kamar yadda ya kasance daga cikin jagororin juyin juya halin muslunci a kasar ta Iran.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!