Shekarar 2020 Ta Zo Da Abubuwan Ban Mamaki A Harkar Wasannin Kwallon Kafa

2021-01-02 09:01:04
Shekarar 2020 Ta Zo Da Abubuwan Ban Mamaki A Harkar Wasannin Kwallon Kafa

Za a iya cewa shekarar 2020 tazo da abubuwan ban mamaki wadanda babu wanda yayi zaton su a shekarar 2020 kuma tunani ba zai taba kawowa zasu faru ba musamman buga wasan kwallon kafa babu ‘yan kallo.

Shekara ta 2020 ta zama mai cike da kalubale a fadin duniya har da bangaren wasanni, bayan da cutar korona ta dagula al’amura a fadin duniya sannan ta tsayar da abubuwa da dama ciki kuwa hard a wasannin kwallon kafa.

Cutar ta sa an dauke wasu wasannin daga lokacin da aka tsara zuwa wani lokacin nan gaba, sannan kuma an koma buga wasu ba magoya baya, bayan da wasu kungiyoyin suka bukaci ‘yan wasa su rage albashi, wasu ma suka yafe na wasu watannin a wasu kungiyoyin musamman a kasar Sipaniya da Faransa.

Cikin shekarar nan fitattun ‘yan wasa sun mutu da suka hada da Diego Maradona da Kobe Bryant da sauransu sannan duk da bullar cutar korana an ci gaba da wasanni, bayan da aka dauki matakan hana yada annobar, hakan ya sa an samu ‘yan wasa da kungiyoyi da jami’ain da suka taka rawar gani a shekarar 2020.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!