​Rauhani: Tabbas Iran Za Ta Dauki Fansa Kan Kisan Qassem Sulaimani

2021-01-01 15:46:50
​Rauhani: Tabbas Iran Za Ta Dauki Fansa Kan Kisan Qassem Sulaimani

Shugaba Rauhani na Iran ya jaddada cewa, Iran tana nan kan bakanta na daukar fansa a kan kisan Kasim Sulaimani a lokacin da ya dace.

A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yau a birnin Tehran, Shugaba Hassan Rauhani ya jaddada cewa, batun daukar fansa a kan kisan Sulaimani babu makamawa a cikinsa, magana ce kawai ta lokaci.

Ya ce a cikin shekarun da Donald Trump ya yi yana mulkin Amurka ya tafka manyan laifuka da dama a kan al’ummomin duniya, wanda kuma Iran na daga cikin kasashen da ya tafka laifuka a kanta, daga ciki har da kakaba wa kowane bangare na kasar takunkumi da nufin karya ta.

Rauhani ya ce, mulkin Trump ya yi kama da mulkin Saddam Hussain a Iraki, wanda ya yi amfani da damar da ya samu ta mulki wajen cutar da wasu, wanda Amurka ce kuma ta bashi dukkanin kariya domin yin mulkin kama karya, ta gama cin moriyarsa kuma ta yi watsi da shi.

Rauhani ya bayar da misalign kallafaffen yakin da Saddam ya dora wa Iran har tsawon shekaru 8, yayin da shi kuma Trump ya dora wa Iran matsanancin takunkumi na tsawon shekaru 3 na mulkinsa, sannan wani laifi mai girma da ya aikata mafi muni a kan sauran ayyukan, shi ne kisan Kasim Sulaimani da Abu mahdi Almuhandis.

Shugaban na Iran ya ce kamar yadda Saddam ya yi ya gama ya tafi, shi ma Trump a yau kwanaki 20 ne suka rage masa a rayuwarsa ta siyasa, daga nan kuma ya shiga kwandon shara.

Haka nan kuma shugaba Rauhani ya kara jaddada cewa, dukkanin wadanda suke da hannu a kisan kasim Sulaimani martanin Iran zai shafe su, daga ciki kuwa har da wadanda suka bayar da umarnin kisan, da kuma wadanda suke da hannu wajen aiwatar da shi, wadanda a halin yanzu an gano adadi mai yawa daga cikinsu.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!