Yemen: Gwamnatin San’a Ta Ce Harin Aden Rikicin Cikin Gida Ne Tsakanin ‘Yan Mamaya

A cikin bayanin da gwamnatin San’a
ta fitar ta bayyana cewa, wannan hari ya auku ne sakamakon irin matsanancin
sabanin da ke tsakanin ‘yan mamaya da suke hankoron mamaye kasar Yemen, da kuma
wasu ‘yan kasar da suke mara musu baya saboda abin duniya.
Harin dai ya auku ne a lokacin da
tawagar gwamnatin hadio Mansur mai matsugunni a kasar saudiyya ta iso birnin
Aden da ke kudancin Yemen, inda isowar jirgin da ke dauke da su ke dawuya, sai
manyan bama-bamai uku suka tarwatse a wurin, lamarin da ya yi sanadiyyar
mutuwar mutane fiye da ashirin wasu da dama kuma suka jikkata.
Gwamnatin Hadi Mansur ta tuhumi
kungiyar Ansarullah ko kuma Alhuthi da kai harin, amma kungiyar ta mayar da
martani da cewa, su dai nemi wadanda suka kai harin yaka junansu.
Kakakin gwamnatin San’a Shami
Daifullah ya bayyana cewa, musayar wuta da aka samu tsakanin jami’an tsaron
gwamnatin Hadi da wadanda suke tare da su a filin jirgin, ya kara tabbatar da
cewa rikicin na cikin gida ne a tsakaninsu.
Hadi Mansur da ya tsere daga Yemen
zuwa birnin Riyad na Saudiyya, inda ya kafa gwamnati a can da ke da
matsugunni a cikin manyan otel-otel na birnin Riyad.
015