Syria Ta Bukaci MDD Ta Dakatar Da Hare haren Isra’ila

2020-12-31 21:52:57
Syria Ta Bukaci MDD Ta Dakatar Da Hare haren Isra’ila

Kasar Siriya ta bukaci MDD, da ta, dakatar da hare haren da yahudawan mamaya na Isra’ila ke kaiwa kasar na tsawon shekaru.

Ma’aikatar harkokin wajen Syria ta bukaci kwamitin sulhun MDD da ya dauki matakan gaggawa don dakatar da munanan hare haren da Isra’ila ke kaiwa kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar na SANA ya ambato.

A sanarwar, ma’aikatar ta ce hare haren da Isra’ila ta kaddamar suna faruwa ne sakamakon goyon baya marar adadi da kasar Amurka da wasu mambobin kwamitin sulmin MDD ke bayarwa.

A wasu alkalumma data fitar ranar ALhamis rundinar sojin Isra’ila ta ce ta kai hare hare 50 a Siriya a cikin shekara 2020.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!