Tawagar Sulhu Ta MDD, Ta Fara Janyewa Daga Sudan

2020-12-31 21:47:37
Tawagar Sulhu Ta MDD, Ta Fara Janyewa Daga Sudan

Tawagar hadin guiwa ta wanzar da zaman lafiya ta MDD, da tarayyar Afrika a yankin Darfour na Sudan ta kawo karshen aikinta a hukumance a wannan Alhamis.

Tawagar ta (Minuad), ta shafe shekara 13 a yankin na Darfour dake yammacin kasar ta Sudan mai fuskantar rikice rikicen kabulanci.

Bayan ficewa daga yankin tawagar za ta mika aiki tabbatar da tsaron fararen hula a yankin ga gwamnatin Sudan.

Kimanin mambobi 8,000 tawagar ta Minuad ta kunsa da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da kuma fararen hula, wanda kuma zasu fara janyewa daga watan Janairu na shekara mai shirin kamawa, kuma aikin janye tawagar zai dauki tsawan watannin shida.

Saidai mazauna yankin na nuna fargaba game da makomar rayuwarsu bayan janyewar tawgawar, inda ko a makon da ya gabata saidai suka gudanar da zanga zangar kan batun janyewar tawagar ta wanzar da zaman lafiya a yankin ta (Minuad).

Ko baya ga hakan kasashen yamma mambobin kwamitin tsaron MDD, sun nuna damuwa akan janye tawagar da wuri-wuri.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!