Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Yi Maraba Da Allurar Rigakafin Corona Da Iran Ta Samar

2020-12-31 15:09:04
Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Yi Maraba Da Allurar Rigakafin Corona Da Iran Ta Samar

Kakakin hukumar lafiya ta duniya ne ya bayyana jin dadinsu akan samar da allurar rigakafin cutar corona ta Iran, tare da cewa suna jiran samun sakamakon da za a samu daga gwajin.

A jiya Alhamis ne dai hukumar lafiyar ta kasa da kasa ta kuma bayyana cewa; Dacen da masanawa Iraniyawa su ka samu na kirkirar rigakafi, sheda ce akan cewa za mu iya cin karfin wannan annobar ta hanyar samar da rigakafi.

A shekaran jiya Talata ne dai aka fara gwajin allurar rigakafin cutar ta corona wacce masanan Iran ne su ka samar da ita.

An yi gwajin na farko ne dai akan diyar wanda ya jagoranci samar da allurar rigakafin.

Har ila yau an yi wa wasu jami’an cibiyar da ta samar allurar rigakafin, allurar gwajin.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!