Al’ummar Kasar Nijar Suna Ci Gaba Da Sanya Idanu Domin Jin Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisa

2020-12-31 15:04:53
Al’ummar Kasar Nijar Suna Ci Gaba Da Sanya Idanu Domin Jin Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisa

A ranar Lahadin da ta gabata ne da mutanen da su ka kai miliyan 7.4 su ka kada kuri’ar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a cikin mazabu 26,000 a fadin kasar. Da akwai ‘yan takarar shugabancin kasa 30 da su ke son zaman kan kujerar shugabancin kasar.

Dangane da zaben ‘yan majalisar dokoki kuwa, da akwai ‘yan takara 4,205 da suke gogayya da juna akan kujeru 171 na majalisa.

Muhimman ‘yan takarar shugabancin kasar dai su ne Muhammad Bazoum na jam’iyyar ( PNDS-Tarayya), sai Muhammad Ousmane, na jam’iyyar ( RDR Chanji) da kuma Seni Umaru na jam’iyyar ( MNSD).

Rahotanni sun ambaci cewa al’ummar kasar sun fito kwansu da kwarkwatarsu a lokacin zaben.

Kungiyoyi daban-daban da su ka sanya idanu akan zaben sun yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Idanun al’ummar kasar sun nuna kan hukumar zaben kasar ta CENI domin ta sanar da sakamakon zaben, saboda a wuce wajen a shiga wata sabgar.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!