Kiyayyar Dake Tsakanin ‘Yan Nigeria Ta Yi Yawa Da Bai Kamata Su Rike Makamai Ba

2020-12-31 14:56:52
Kiyayyar Dake Tsakanin ‘Yan Nigeria Ta Yi Yawa Da Bai Kamata Su Rike Makamai Ba

Wani shugaban al’ummar Iwo a Nigeria kuma basaraken gargajiya, Abiola Ogundokun ne ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Yadda ‘Yan Nigeria ba su ga maciji da juna, ya kamata gwamnati ta hana daidaikun mutane mallakar makamai.

Basaraken ya kara da cewa, bai wa daidaikun mutane lasisin mallakar makamai zai iya jefa kasar cikin hatsaniya fiye da wacce ake da ita yanzu.

Basaraken ya kara da cewa; “Yan Nigeria ba su da isasshiyar da’ar da za su iya mallakar makamai, saboda kiyayyar da suke yi da juna.

Wani sashe na jawabin Abiola Ogundokun ya bayyana cewa; Da akwai makirce-makirce da ake kitsawa Nigeria, don haka da akwai bukatar duk masu hannu da shuni a wajen tafiyar da kasar da su yi namijin kokari domin dawo da tsaro da zaman lafiya a kasar.

013Comments(0)
Success!
Error! Error occured!