​Lavrov: Rasha Da Iran Za Su Ci Gaba Da Fadada Ayyukansu A Bangaren Soji Da Cinikin Makamai

2020-12-30 21:19:41
​Lavrov: Rasha Da Iran Za Su Ci Gaba Da Fadada Ayyukansu A Bangaren Soji Da Cinikin Makamai

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, kasashen Rasha da Iran za su ci gaba da kara fadada ayyukansu a bangaren harkokin soji da kuma cinikin makamai.

Lavrov ya bayyana hakan ne a yau a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Moscow na kasar Rasha, inda ya jaddada cewa, kasashen Rasha da Iran suna da cikakken hakki na yin mu’amala a dukkanin bangarori na cinikin makamai.

A lokacin da aka tambaye shi kan batun yiwuwar Iran ko za ta sayi wasu manyan makamai daga Rasha, da suka hada har da jiragen yaki samfurin Su-30, da kuma tankokin T-90, Lavrov ya amsa da cewa, a halin yanzu babu wani kaidi a kan Iran na hana ta saye ko sayar da makamai.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin kasar Rasha ta sanar da cewa, bayan janye takunkumin hana Iran saye da sayar da makamai, a halin yanzu kofa bude take a tsakanin kasashen biyu domin ci gaba da kara karfafa alakarsu a wannan bangare.

A ranar 18 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai wa’adin takunkumin Majalisar dinkin duniya na hana Iran saye da sayar da makamai ya zo karshe, inda a halin yanzu kasar tana hakkin sayen kowane irin makami take bukata daga waje, kamar yadda ita kuma za ta iya sayar da nata makaman da take kerawa ga duk kasar da ta ga dama.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!