​Falastinawa Sun Kai Karar Isra’ila Ga Majalisar Dinkin Duniya

2020-12-30 20:20:06
​Falastinawa Sun Kai Karar Isra’ila Ga Majalisar Dinkin Duniya

Gwamnatin Falastinu ta kai karar Isra’ila ga majalisar dinkin duniya kan tsananta hare-haren da take yi a kan al’ummar Gaza.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, Rayad Mansur wakilin Falastinu a mjalisar dinkin duniya ya fadi yau Laraba cewa, sun aike da wasiku guda uku zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, da kuma shugaban kwamitin tsaro, gami da shugaban babban zauren majlaisar.

Ya ce dukkanin wasikun guda uku suna magana ne kan abu guda, wato neman majalisar dinkin duniya kan ta gaggauta daukar mataki na takawa Isra’ila burki, kan hare-haren da take kaddamarwa da jiragen yaki a kan al’ummar yankin zirin Gaza.

Baya ga haka kuma, wasikar ta bukaci dukkanin bangarori na majlaisar dinkin duniya da su sauke nauyin da ya rataya a kansu dangane da ci gaba da gina matsugunnan yahudawa da Isra’ila take a cikin yankunan Falastinawa, musamman a birnin Quds.

Wakilin na Falastinua majalisar dinkin duniya ya jaddada cewa, ci gaba da kisan Falastinawa da Isra’ila ke yi, da kuma ammaye yankunansu tare da gina matsugunnan yahudawa a ciki ba tare da duniya ta taka mata burki ba, babban abin kunya ne ga majalisar dinkin duniya, da dukkanin kasashe masu da’awar kare hakkin bil adama a duniya.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!