Rauhani: Ci Gaban Da Iran Take Samu A Fagen Fasahar “Nano” Abin Alfahari Ne

2020-12-30 08:55:13
Rauhani: Ci Gaban Da Iran Take Samu A Fagen Fasahar “Nano” Abin Alfahari Ne

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani da ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa wajibi bangarori masu zaman kansu su shiga cikin wannan fage domin su taka rawa.

Shugaba Rauhani ya kuma yi ishara da yadda ake amfani da wannan fasaha a fagage daban-daban na sana’o’i, kiwon lafiya da ilimomi mabanbanta da suka hada da ilimin sararin samaniya.

Wani sashe na jawabin shugaban kasar ta Iran ya ce; A wannan lokacin da ake ciki ci gaban Iran a fagen fasahar Nano, bai tsaya a cikin rubuta kasidu ba kadai, ya mayar da shi zuwa sana’a da kere-kere.

Da yake Magana akan takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, shugaban na kasar Iran ya ce; Takunkuman ba su tsaya akan kayan da Iran din take shigo da su ba,hadda wadanda take fitar da su zuwa kasuwannin duniya.

Shugaban na Iran ya yi kira ga bangarori masu zaman kansu da su shigo cikin fagen fasahar “Nano” domin zuba hannun jari a ciki.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!