Syria: Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-hare A Kusa Da Birnin Damascuss Na Kasar Syria

2020-12-30 08:52:06
 Syria: Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-hare  A Kusa Da Birnin Damascuss Na Kasar Syria

Kamfanin dillancin labarun Syria ( SANA) ya nakalto majiyar tsaron kasar na cewa; Na’urorin tsaron sama na kasar Syria, sun kakkabo makamai masu linzami da dama da sojojin HKI su ka harba a yanklin “Nabi Habil’ a Zabadany, da ke kusa da birnin Damascuss.

Majiyar ta kara da cewa; Da misalin karfe 1;30 na safiyar yau ne abokan gaba su ka ka hari ta sama da makamai masu linzami akan yankin Nabi Habil a bayan garin Damascuss.”

Bugu da kari majiyar ta ce; Na’urori tsaron sama na Syria sun kakkabo makamai masu linzami da dama na abokan gabar.

Sai dai kuma wasu soja daya yayi shahada yayin da wasu 3 su ka jikkata.

Tun bayan da Syria ta fada cikin yaki a 2011 ne dai ‘yan sahayoniyar suke kai ma ta hare-hare daga lokaci zuwa lokaci da hakan kan yi sanadiyyar shahdar sojoji da fararen hular kasar.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!