Iraniyawa 4 Ne Suke Takarar Zama Mafificin ‘Yan Wasa Na Asiya A 2020 Mai Karewa

2020-12-30 08:49:19
 Iraniyawa 4 Ne Suke Takarar Zama Mafificin ‘Yan Wasa Na Asiya A 2020 Mai Karewa

Tashar talabijin din “Fox Sport” ta kasar Autsria ta bayar da labarin ‘yan wasan nahiyar Asiya da suke takarar zaman mafifitan ‘yan wasa na shekarar 2020 daga cikinsu da akwai Iraniyawa 4.

“Yan wasan Iraniyawa,sun kunshi Muhammad Husain Kan’any Zadikan daga kungiyar wasan kwallon kafa ta Perspolis, Mahadi Darimy, daga kungiyar wasan kwallon kafa ta Rio Api da Porto daga kasar Portugal. Sai kuma Sardar Azmun daga kungiyar kwallon kafa ta Zenith a Rasha,sannan kuma Shuja’a Khalil Zadeh daga Rayyan na kasar Qatar.

Ita kuwa kasar Japan tana da ‘yan wasa 5 da suke takarar, sai Korea ta kudu da ‘yan wasa 4.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!