Gwamnatin Kasar Zimbabwe Ta Fara Dauke Mutane Daga Yankunan Da Ake Tsammanin Isar Mahaukaciyar Guguwa

2020-12-30 08:44:38
Gwamnatin Kasar Zimbabwe Ta Fara  Dauke  Mutane Daga Yankunan Da Ake Tsammanin Isar Mahaukaciyar Guguwa

A jiya Talata ne aka fara dauke daruruwan iyalai daga yankin Chimanimani dake gabashin kasar, gabanin isar mahaukaciyar guguwa ta Chaleni, kamar yadda ma’aikatar watsa labarai ta kasar ta sanar.

Sakataren ma’aikatar watsa labarun Nick Mangwana ne ya sanar da cewa; “gwamnati tana daukar mutanen na yankin Chimanimani ne zuwa yankuna masu aminci saboda kaucewa barnar da mahaukaciyar guguwar za ta iya haddasawa.”

A halin da ake ciki dai guguwar wacce aka bai wa sunan; Chalane, tana kadawa a cikin kasar Mozambique, za kuma ta iya rikidewa zuwa mahaukaciya tare da ruwan sama mai karfi a cikin kasar baki daya, musamman a yankunan gabashin kasar dake kan iyaka.

Da akwai cibiyoyi 20 da gwamnatin kasar ta samar a cikin gundumar Manicaland.

A shekarar da ta gabata mai dubban mutane ne su ka rasa rayukansu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Idai,a kasar da har yanzu wasu daga cikinsu suna rayuwa a cikin hemomi.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!