Kungiyoyin Gwagwarmaya Na Falasdinawa Na Atisayen Soji

2020-12-29 21:36:49
Kungiyoyin Gwagwarmaya Na Falasdinawa Na Atisayen Soji

A karon farko, kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun gudanar da wani atisayen soji na hadin guiwa a zirin Gaza.

Atisayen wanda aka kwashe sa’o’I anayinsa a yau Talata, na tunawa ne da yakin 2008 da yahuadawan mamaya na Isra’ila.

Yayin atisayen gungun kungiyoyin sun yi ta harba rokoki zuwa cikin tekun mediteranien.

Wani kakakin rundinar Al’Quds, ya bayyana atisayen da hadin kai dake akwai tsakanin kungiyoyin na gwagwarmaya domin tunkarar duk wata irin barazana daga Isra’ila.

A ranar 27 ga watan Disamba na 2008 ne, Isra’ila ta kaddamar da wani gagarimin farmaki na sama da kasa a zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 1,440.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!