RSF : ‘Yan Jarida 50 Aka Kashe A Cikin Shekarar 2020

2020-12-29 21:33:33
RSF : ‘Yan Jarida 50 Aka Kashe A Cikin Shekarar 2020

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa (RSF), ta fitar da rahoton dake cewa ‘yan jarida 50 ne suka gamu da ajalinsu a cikin shekara 2020 din nan mai shirin karewa.

A rahoton na shekara shekara kungiyar ta ce bakwai daga cikin goma na ‘yan jaridan an kashe su ne a kasashen da ake zaman lafiya ba wai masu fama da yaki ba.

Rahoton ya ce idan an samu raguwar ‘yan jaridan da aka kashe idan aka kwatanta da shekara 2019, inda ‘yan aka kashe ‘yan jarida 53, to yawan ‘yan jaridan da aka kashe a kasashen da ake zaman lafiya na da matukar daukan hankali.

Yawan ‘yan jaridan da aka kashe a yankunan dake fama da yaki ya ragu da kashi 58 cikin dari a shekara 2016, zuwa kashi 32 cikin dari a bana a kasashen Siriya da Yemen.

A Mexico ne aka fi kashe ‘yan jarida a bana inda aka kashe guda takwas, sai Indiya (4), Pakistan (4), sai kuma Philippines (3), da Honduras (3), wasunsu ma a cewar rahoton kisan walakanci aka masu.

Baya ga ‘yan jaridan da aka kashe, akwai wasu 387 da aka jefa gidan kurkuku a cewar rahoton na RSF.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!