Ana Ci Gaba Da Jiran Sakamakon Zabe A Jamhuriyar Nijar

2020-12-29 21:26:54
Ana Ci Gaba Da Jiran Sakamakon Zabe A Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, ana ci gaba da jiran sakamakon zaben shugaban kasar da aka kada kuri’arsa a ranar Lahadi data gabata.

A jiya Litini dai hukumar zaben kasar ta fara fitar da sakamakon zaben wucin gadi na yankunan farko farko data samu.

Ye zuwa ranar Alhamis ne ake sa ran samun gabadayen sakamakon zaben.

A sakamakon zaben shugaban kasa daga kananen hukumomi 23 daga cikin 266 da aka fitar a ranar Litini, dan takarar jam’iyyar PNDS-tarayya mai mulki ne Malam Bazoum Mohamed ke kan gaba, sai kuma tsohin shugaban kasa Mahamane Usman dake biye masa, wadanda dama su ne manyan ‘yan takara a zaben.

Kafin nan dai masu sanya ido na kasa da kasa a zaben sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!