Juventus Na son Sayen Pogba Na Manchester United

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta bayyana aniyarta ta sayan
dan wasan Manchester United Paul Pogba amma akan kudi fam miliyan 50 saboda
yadda kungiyoyi suke rashin kudi sakamakon cutar Korona wadda ta addabi duniya.
Tuni
dai rahotanni suka bayyana cewa Juventus tana son dawo da dan wasan idan har
Manchester United zata amince da musayar ‘yan wasa saboda Juventus tana son
bayar da dan wasanta Paulo Dybala domin karvae Pogba idan har Manchester United
ba zata karvi fam miliyan 50 ba.
Amma
kuma mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafan ta Manchester United, Ole
Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa dan wasa Paul Pogba yana cikin farin ciki a
kungiyar kuma zai bawa duniya mamaki daga yanzu har zuwa karshen kakar wasa ta
bana.
Idan baku manta ba a kwanakin baya wakilin Pogba kuma mai kula
da harkokin wasanninsa, Mino Rioala ya bayyana cewa Pogba baya jin dadin zama a
Manchester United sannan kuma ya kamata ya sauya kungiya a watan Janairu ko
kuma a karshen kakar wasa ta bana.
A
watan Yunin shekara ta 2022 kwantiragin dan wasan tawagar Faransan zai kare,
zai kuma iya barin Old Trafford a watan Janairun shekara ta 2022 a matakin
wanda bai da yarjejeniya kuma Pogba mai shekara 27, ya buga wasanni 12 a gasar
Premier League har da shida da aka fara bugawa da shi a fili a kakar bana.