Iran: An Fara Gudanar Da Gwajin Allurar Rigakafin Corona Akan Mutane A Yau Talata

2020-12-29 15:08:24
Iran: An Fara Gudanar Da Gwajin Allurar Rigakafin Corona Akan Mutane A Yau Talata

Sa’o’i kadan da su ka gabata ne dai aka fara yin allurar rigakafin ta gwaji akan wata mace, an kuma gama ba tare da wata matsala ba.

Da akwai mutane da dama da suka gabatar da kawunansu domin ayi gwajin allurar rigakafin da su

Kwamitin da yake aiwatar da umarnin Imam Khumaini ( R.A.) ne ya samar da rigakafin, kuma gwajin na farko an yi shi ne akan diyar shugaban kwamitin. Wasu daga cikin wadanda aka yi wa allurar rikagafin a yau sun hada da shugabannin kwamitin.

Tun bayan bullar cutar ta corona, Iran ta bude bincike akan hanyoyin samar da rigakafinta, da kuma daukar tsauraran matakai na dakile ta.

A cikin makwannin bayan nan, ana samun koma bayan yaduwar cutar a Iran, haka nan kuma wadanda suke rasa rayukansu saboda ita.


013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!