Shubaban Kasar Burkina Faso Ya Yi Alakwalin Tabbatar Da Tsaro A Kasar

2020-12-29 15:04:11
 Shubaban Kasar Burkina Faso Ya Yi Alakwalin Tabbatar Da Tsaro A Kasar

Shugaba Roch Marc Christian Kabore wanda aka sake zabarsa a zango na biyu na shugabancin kasar ta Burkina Faso, ya ce sake dawo da tsaro a kasar shi ne zai zama abu mafi muhimmanci da zai sa a gaba.

A jiya Litinin ne dai Kabore dan shekaru 63 ya yi rantsuwar sake kama aiki na shugabancin kasar a karo na biyu a cikin filin wasan kwallon kafa na birnin Ouagadougou.

Shugabannin kasashen Afirka 10 ne su ka sami halartar binin, da kuma bakin da suka kai 1,200.

Kabore ya yi furuci da barnar da masu kai hare-hare a kasar su ka yi, wadanda su ka ketaro daga kasar Mali mai makwabtaka da Burkina Faso.

Akalla mutane 1,200 ne aka kashe, yayin da wasu miliyan daya su ka yi hijira daga gidajensu saboda kaucewa fadace-fadace.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!