An Yaba Da Yadda Aka Gudanar Da Manyan Zabukan Kasar Niger

2020-12-29 14:55:47
An Yaba Da Yadda Aka Gudanar Da Manyan Zabukan Kasar Niger

Shugaban tawagar gamayyar kungiyar masu sanya idanu akan zaben na Nijar, Mr. Dambagi Son ya yaba da yadda zaben ya kasance duk da cewa an sami kananan matsaloli nan da can.

Kungiyar da aka fi sani da ( MOE-COCEN) ta aike da masu sa idanu 750 a cikin sako-sako na kasar a ranar zabe.

Kungiyar ta bi diddigin yadda zabukan kasar su ka kasance a cikin mazabu 484 da su ka hada a cibiyoyi 311 masu kula da yadda harkar zaben take tafiya.

Kakakin kungiyar ya ce; An yi zaben a cikin wata na 12 a cikin ruwan sanyi a cikin dukkanin inda aka sanya idanu.”

A ranar 27 ga watan nan na Disamba ne dai aka gudanar da zaben na shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisar dokokin kasar ta jamhuriyar Nijar.

Manyan ‘yan takrarar shugabancin kasar dai su ne; Muhammad Bazoum na jam’iyyar PNDS tarayya ta shugaba Muhammadu Issoufu. Sai kuma Seyni Umaru na jam’iyyar MNSD, sannan tsohon soja Saliou Djibo.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!