Iran Za ta Mayar Da Martini Mai Tsanani Kan Duk Wani Gigin HKI A Tekun Fasha

2020-12-29 11:15:11
Iran Za ta Mayar Da Martini Mai Tsanani Kan Duk Wani Gigin HKI A Tekun Fasha

Kakakin kwamitin tsaron kasa da manunofofin kasashen wajen na majalisar shawarar musulunci ta Iran Abolfazl Amuyi ya fadi cewa HKI ta kwan da sanin cewa Iran ta shirya tsaf don mayar da martini mai tsanani game da duk wani gigi ko wuce gona da iri da za ta yi kan kasarmu.

Wannan yana zuwa ne bayan da jaridar washington Post ta buga wani labari da ke nuna cewa jiragen ruwa na yaki na HKI sun nufin yankin tekun Fasha a matsayin wani gargadi ga kasar Iran da kuma shirin da Isra’ila take da shi wajen fara duk wani yaki idan haka ta taso.

A cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin din Aljazeera ta kasar Qatar Amuyi ya fadi cewa Isra’ila tana neman wata dama ce da za ta fake da ita domin jefa yankin cikin tashin hankali a ranakun karshe na karshen mulkin shugaban Amurka Donald Trumph.

Ko a yan kwanakin nan ma kakakin sojojin HKI Hidai Zilberman ya fadawa wata jaridar Elaph News ta kasar Saudiya cewa suna bibiyar yanayin motsin kasar Iran a yankin baki daya, kuma jiragen ruwanta suna ci gaba da shawagi da zuba ido a ko ina a yankin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!